ABU-MALEEK CHAPTER 10 BY Nimcyluv

ABU-MALEEK CHAPTER 10 BY Nimcyluv

             Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sama da rigar jikinta, tare da ƙoƙarin kunce igiyar da aka ɗaure mata ƙirji da ita.

Wani masifafan ihu Julde ta sanya, saboda tsananin tsoran daya shigeta,

Ta shiga kare ƙirjinta da dukkan hannayenta, Jikinta duk rawa yake, cikin rawar murya da gigita tace.

“Waye kai? Me kake so? Noi indema?”

Ta jera masa tambayar lokacin, saboda jin wanda ya Shigo ɗin yayi shiru,

Gashi yana ƙoƙarin yi mata tsirara, Barkido kam tuni ya fara fidda numfashi yana sakin Ajjiyar zuciya saboda santala santalan cinyoyinta da suka bayyana,

Duk da cewa warin dauɗa take amma hakan bai hana cinyarta yin wani kyau ba,

Ganin tana shirin bashi wahala kawai ya sanya hannunsa tare da kama kanta ya gwarata da bango,

Wani gigitaccen ihu ta sanya lokaci guda kuma jini ya ɓalle daga goshinta ya shiga zuba yana sauka zuwa saman fuskarta,

Kafin ta sulale a wajan babu numfashi, wani irin Murmushin jin daɗi yay kana ya miƙe ya shiga ƙoƙarin zame kayan jikinsa,

Da wani irin sauri Barkido yaja baya tare da ɓoyewa a bayan ƙofar bukkar, hakan ya faru ne saboda jiyo Muryar Madibbo yana faɗin.

“War Julde, Hai kazo kana ina?”

Ya faɗa yana leƙawa tare da ƙarasawa inda ya hangi Julde kwance dafe da ƙirjinta babu numfashi,

Da wani irin saurin gigita Madibbo ya ƙarasa shiga cikin bukkar tare da nufar inda Julde ke kwance,

Yana shiga Barkido ya fita da sauri yana Murmushin jin daɗin babu wanda ya kansa.

Jawo Julde yayi jikinsa yana jijjiga ta tare da kiran sunanta, ganin ko motsi ba tayi yasa Madibbo faɗin.

“Ko dama ta maa?” (Meke damunki?”

Da sauri kuma ya kwantar da ita tare da fita da sauri ya nufi inda yake ɓoye, Ɓoyayyan Sirrin da yake ɓoyewa Julde daman irin wannan ranar yake jira,

Wacce ta tazo ya faɗa Julde komai dake faruwa Wanda bata san shi ba.

Yana fita ya nufi can wata ƙuryar duhuwa duk da cewa dare ne Amma haka ya shiga cikin duhuwar tare da haƙe ƙasar ramin daya ɓoye abun.

Yana gama tunuwa ya miƙe da sauri tare da fara tafiya ya nufi cikin Rugar,

Murmushi Arɗo da Lamiɗo sukai, a hankali kuma Arɗo ya saki wani zabgegen Maciji dake hannunsa zuwa ƙasa,

Kai tsaye macijin kuma wajan Madibbo yayi saboda yaga gilmawarsa,

Sosai Madibbo ke sauri domin ya isa ga Julde ya faɗa mata shuɗɗaɗan tarihin daya huce kafin Zuwan wannan ranar.

Kamar daga sama yaga saukar Macijin a gabansa yana sara kai tare da fiddo da harshen bakinsa, ya shiga wa yiwa Madibbo tsartuwa,

Wani irin kyarma jikin Madibbo ya ɗauka, gashi ya kasa koda mutsawa, tsoro da gigita suka cika masa zuciya.

Wani irin tsalle Macijin yayi tare da.

   *Daga wannan page ɗin na gama free pages, sabida halin rashi da ake ciki na raba tsarin biyan gida biyu, 500 for VIP posting safe da yamma, 300 for nrml grp, posting idan anyi yau babu gobe👏🏻 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616*

Sarawa Madibbo bakinsa a dai-dai satin ƙahon zuciyarsa, nan take kuma Madibbo ya faɗi yana fitar da wata iriyar kumfa daga cikin bakinsa,

Kullin abinda ke hannunsa wanda yake son faɗawa Julde ya ƙwace daga hannunsa tare da faɗuwa ƙasa,

Ɓat kuma kamar Aljani Macijin ya ɓace daga wajan,

Kakarin mutuwa Madibbo ya fara idanunsa ya shiga lumshe bakinsa ɗauke da sunan JULDE,

Arɗo da Lamiɗo ne suka ƙarasa inda yake kwancan tare farayi masa dariya,

A hankali kuma Lamiɗo ya ɗauki kullin ba tare daya buɗe yaga ko menene ba, ya cilla kullin sama,

Kana sukai gaba Abunsu cike da farin cikin samun nasarar raba Madibbo da ransa,

Bakinsa ɗauke da salati Ubangiji ya amshi ran Madibbo.

Sanyin safiya mai cike da dadɗar iska ne ya farkar da Julde daga suman da tayi,

Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya ta sauke, tare da runtsa idanunta wanda suka kumbura saboda kuka, ga kuma rashin wadatacciyar lafiya da idanun yake da shi,

A hankali ta miƙe zaune tare da kifa fuskarta a tsakanin zuciyoyinta ta saki wani irin raunataccen kuka!

Hakiƙa tana buƙatar mataimaki a rayuwarta, amma waye zai zama gatanta? Waye zai zama Garkuwa a gareta? Waye zai zama tubalin da zai gina mata sabuwar rayuwa harta mata da wannan rayuwar da take mata ƴanci?

Waye zai zama Muradin ranta? Wanda zai zama madubi abin haska zuciyarta? Ko dai TABI ABINDA ZUCIYAr take faɗa mata ne?

Kuka take mai cike da ladamar rayuwa ƙunci kuma da baƙin ciki,

Ganin bata da wani gata sai Allah, bata da wanda zaice mata tayi shiru ya sanya ta sassauta kukan tare da ɗaukan sandar ta, ta shiga laluban hanya idanunta na ɗan juyawa,

A haka ta samu ta fita daga cikin Bukkar hannunta ɗauke da ruwa,

Can bayan Bukkar ta tsuguna tare dayin fitsari kana tayi alwala ta koma bukkar tare da gabatar da sallah bayan ta yane kanta da wani siririn abu.

Tana idarwa ta fara jin surutai bata motsa ba, sai da taji ana faɗin Madibbo ya mutu, kusan mutuwar tsaye tayi, jinta da gaba ɗaya ya ɗauke, bugawar da zuciyarta take ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙo,

Farkawa tayi ta kanta kwance ashe tun a lokacin ta suma sabida trumer ɗin data shiga.

Yini tayi kuka babu abinda ke tsayar da ita sai Sallah, daman sallar ba wata iyawa tayi ba sosai, bare kuma ta iya yiwa mamaci addu’a,

Haka ta ƙara kwanciya bacci banda ruwa babu abinda yake cikinta,

Ji take kamar itama tamar Duniyar ko zata huta, idan tana da rabon jin daɗi a lahira sai ta samu,

Washe gari da safe, Arɗo ya sanya wasu mutane zuwa su tafi da ita, kwallon ta Arɗo yayi yace.

“Wato kai yaron nan bakaji ko? Haii sai da ka sake sace mana nonon nagge ko? Gashi dalilin hakan ka sanya Nagge ya mutu”

Jikin Julde ya ɗauki rawa, domin ba zata mance da cin zarafin da akai mata na aski ba, ga azabar da aka gana mata na murje mata nono,

Kuka ta sanya ta shiga rarrafawa duk da bata ganin kowa amma a haka ta ƙarasa gaban Arɗo tare da riƙe masa ƙafa tace.

“Kayi min rai Arɗo, kada ko sake murje min nono, da ƙyar nake numfashi saboda abinda kuka sanya Min, Aradon Allah ban saci komai ba”

Da sauri Lamiɗo yace.

“Arado ƙarya ka, Arɗo zai maka ƙarya? Da kanshi ya ganka kana tatse mashi nono, dole ka kiwata mana Nagge guda ɗari bisa abinda ka aikata”

Zuciyar Julde ta buga da ƙarfi Tayaya zata iya kiwo? Tayaya ne zata iya kula da Nagge guda ɗari?”

Gaba ɗaya wajan suka sanya ihu akan dole Julde tayi masu kiwo ai tana sandar ganin hanya,

Arɗo ne yayi gyaran murya yace.

“Maza ki haɗa mana Nagge guda ɗari a fito dasu daga garke yanzun nan, kuma kada ka sake a rasa guda ɗaya idan hakan ya fara to walle kai ma saika matu”

Allah sarki baiwar Allah bata da wata mafaka dole tabi abinda sukace mata,

Yin kiwon ma zai sanya tana samun abinci ci,

Haka ta tisa Nagge guda ɗari a gaba zuwa daji, tana dafe da ƙirjinta da yayi mata wani irin nauyi, da ƙyar take jan numfashi,

Tana zuwa wata ƙorama taja ta tsaya tare da kwanciya wajan ruwa ko taji sauƙi daga azabar da ƙirjinta yake mata gaba duniyar tayi mata zafi,

Ajjiyar zuciya ta sauke tana ƙara riƙe ƙirjinta a haka wani wahalallan bacci ya ɗauke ta.

Slowly ya shiga ɗaga eyes lashes ɗin idanunsa, wanda suke zara-zara sunyi kwance luff saman fatar idanunsa,

Tun bayan yayi sallah ya koma bacci sai yanzu ya samu zarafin tashi daga nauyayyen baccin daya ɗauke sa,

Ƙuri yayiwa tafkeken photon Queen Roomana wacce take sanye da milk ɗin voyal ta ɗura light blue ɗin Alƙyabba, wacce tai mata kyau sosai,

Tayi Murmushi wanda ya haddasa fitowar teeths gave ɗinta irin na Abu Maleek,

Idanunsa yaja ya rufe ya yana taune leɓansa a hankali ya shiga sauke ajjiyar zuciya, ɗan ware gajiyayyun idanunsa yayi sabida motsin da yaji,

Yana juyawa idanunsa ya sauka kan MALEEK dake tsaye rungome da Sweet,

Da sauri ya juya kansa yana rufe idanunsa,

Shi sam ya manta da batun cewa Maleek ɗin yana sashinsa,

A duk sanda yay arba dashi sai yaji zuciyarsa ta buga,

Kuma yana ɗaya daga cikin dalilin daya sanya yabar ƙasar baki ɗaya,

Miƙewa yayi a hankali yana ɗan kwaɓe fuska ganin hakan yasa Maleek matsawa kusa dashi yace.

“Èkaro Bàami” (ina kwana Baba?)

Fesar da iska Abu Maleek yayi ba tare daya amsa gaisuwa ta Maleek ɗin ha yayi gaba zuwa toilet,

Ganin hakan ya sanya Maleek sakin Sweet tare da buɗe baki ya sanya kuka yana buga ƙafa,

Cak Abu Maleek ya tsaya kafin a hankali ya sanya hannunsa a saman goshinsa ya shiga murza,

Maleek soyayyyar mahaifin nasa ce ta tare masa a zuciya shiyasa yau yake son kasancewa dashi,

Domin yaji ɗumi irin na mahaifinsa, amma a koda yaushe mahaifin nasa gudunsa yake ba tare daya san dalili ko kuma aibun dake tare dashi ba,

Ganin kukan na Maleek yayi yawa ne yasa a hankali Abu Maleek ya sulale a wajan tare da zama a armchair, yana ware firgitattun idanunsa,

Cikin nutsuwa ya miƙa wa Maleek ɗin hannunsa alamar yazo,

Da gudu ya ƙaraso wajan mahaifin nasa, yana sakin dariya tare da shigewa jikin Jalaluldeen,

Kallon yaron yayi yaga babu wata kama tasa wanda Maleek bai kwashe ta ba tass,

Kenan dalilin daya sanya King Tunde da kuma su Mai Babban ɗaki ƙaunar Maleek ɗin kenan?

Ya tambayi kansa a zuciya, a fili kuma wani ƙaƙƙarfan Numfashi ya sauke, 

Gently kuma ya ɗura softness hands ɗinsa duk biyun a saman sumar Maleek,

Kamar mai koyan magana ya shiga kokawa da laɓɓansa,

Da ƙyar ya samu kalmar.

“Shè layó lábo?” (Fatan kana lafiya?)

Kalmar datai fitar gurbi kenan daga cikin bakinsa ba tare daya shirya hakan ba,

Cikin tsananin farin ciki da kuma jin daɗi Maleek ya rungome Dad ɗin nasa,

Yau rana ce babba a garesa tunda har Abu Maleek ya fito da kansa ya tambayi lafiyarsa,

Cikin soyayya da kulawa Maleek ya ɗan shagwaɓa fuska yace.

“Baàmi baka sona da gaske? Me mayi maka? Kullum kana gudu na, a school kowa Bàami ɗinsa ke zuwa ɗauko sa, amma ni bana ganinka, ina kake ɓoyewa? Meyesa kuma baka sona?”

Ya ƙare tambayoyin nasa idanunsa na zubar da hawaye kasancewar Maleek yaro mai shegen wayo,

Sarawa kansa yayi sabida tambayoyin ba zata da Maleek ɗin ya jefesa dashi, a zahirin gaskiya shima bashi da amsar wannan tarin tambayoyinsu, balle ya bawa Maleek ɗin amsar su,

Shi mamakin surutun yaron yake, ga kuma shegen zaƙin murya kamar tasa, ganin yana shirin yin wata tambayar ne ya sanya Abu Maleek saurin taran Numfashinsa tare da faɗin.

“Ya school?”

Washe baki Maleek yayi yace.

“Ina jin daɗi karatu sosai Bàami, kasan me zan zama idan na girma?”

Girgiza kai Abu Maleek yayi yana mai ɗan ƙara kallon yaron a kaikaice, 

Baya Maleek yayi kaɗan kafin ya shagwaɓe fuska, tare da rausayar da kansa gefe yace.

“O’ohhhh ABU MALEEK”

 Wani Murmushi ne ya suɓuce wa Abu Maleek, wato Maleek yana son buga ƙwallo kenan,

Jinjina kansa yayi tare da Miƙewa ya shafa kan Maleek ɗin,

Ba tare kuma da yace komai ba ya nufi bathroom.

A can shashin King Tunde Muhammad Jalal tuni kowa ya halarci wajan, ana jiran zuwan ABU MALEEK,

Ƙarfe sha ɗaya da ƴan mintuna Abu Maleek ya fito daga sashin sa, bayan ya shiga part ɗin gym ɗinsa,

Cikin nutsuwa haɗi da kamewa Abu Maleek yake taka ƙafafuwansa a ƙasa,

Yana sanye da wata fara jallabiya  talitha kaftan, mai taushi da kuma santsin gaske, sai maiƙo dake sabida santsin yadin jallabiyar,

Jinjina kansa kawai yayi yana sauraran abinda Salimerh take faɗa masa,

Itama cikin wata haɗaɗɗiyar jallabiya ta mata  La Doublej milk colour,

Ta sanya duka hannayenta cikin aljihun Jallabiyar,

Cikin ƙasa da Murya saboda tasa baya son ihu akai, tace..

“Zaki, ka kula dan Allah, kasan kana da matsala kada kace zaka nuna miskilanci a ƙasar daba taka ba, ina jin tsoran wannan tafiyar sosai a raina, amma babu yadda zanyi tunda ka amince da zuwan”

Taune baki yayi yana jin zancan da take wassafa masa, shi surutunta ya bashi mamaki, cai cai cai aita magana,

Ganin yaƙi magana ta marai-raice fuska tace.

“Please Zaki”

Da gajiyayyun idanunsa ya juya ya kalleta ba tare kuma da yace komai ba, ya jinjina mata kansa, a haka suka isa dinning room,

Zama yayi ita kuma ta shiga haɗa masa breakfast wanda Oumuu-Ayman ta bata da kanta, domin babu wanda ta amince ya bawa Abu Maleek ɗin amince,ita take shiga kitchen da kanta ta bashi.

Akara ne, da Ewa Agayin, sai  chicken and waffles with Anadama bread, sosai yaci traditional food ɗin kana ya ɗura da power horse energy mai sanyi,

Sauran tarkacan ko taɓa sa bai ba,

Yana gamawa ya miƙe tsaye, walking slowly ya nufi Sashin King Tunde Muhammad Jalal, a hanya suka haɗu da Junaid kallo guda yayi masa ya ɗauke kai,

Junaid kam ɗan Murmushi yayi idanunsa akan Salimerh wacce tayi masa matuƙar kyau, kamar ya sace ya gudu,

Ba tare shima da yayi Magana ba yabi bayan Abu Maleek yana sakin Murmushi,

Zuwan Abu Maleek ne kuma ya sanya gaba ɗaya mutanan wajan baida idannunsu kansa,

A kullum Abu Maleek sauyawa yake tamkar wanda ya kejin naman mahauniyya,

Yanzu kam zallar kwarjinin sa ne ya baiyana ga kuma wata haiba da izza,

Ba tare daya kalli kowa ba, ya ƙarasa inda King Tunde Muhammad Jalal yake kwance, yana zuwa ya rungome sa sosai tare da tsora masa idanu kamar mai son fahimtar wani abu,

Da wani irin sauri kuma ya.

    *Last free page via 0116886423 sulaiman Naima s union bank*

 

Tallafo fuskar King Tunde yana ƙoƙarin sanya bakinsa cikin na King Tunde domin ya tabbatar da abinda zuciyarsa take zargi,

Da sauri Malamin yace.

“Babu lokaci, gaba ɗaya kwana goma sha biyu ya rage maka, tafiyar kuma tana da tsayi gaske, daga rugar Mahinjo zuwa garin ma sai kayi kwana biyu”

Sauke numfashi yayi a hankali ya zame fuskarsa ba tare daya aiwatar da abinda yake shirin yi ba,

Otun ne yace.

“Za’a sauya maka kama, ta yarda babu wanda zai san cewa kai attajiri ne”

Kallonsu kawai yake ba tare daya ko motsa ba,

Malamin ne ya fito da baƙin fenti da wasu caloli,

Oumuu-Ayman miƙewa tsaye tayi sam zuciyarta ba zata jure hakan ba, Aremo Shakiru da Aremo Adams da Aremo Sharefddeen duk suna zaune ba tare da kowa yace komai ba,

Yaci ace su da suke manya masu ishasshiyyar lafiya sune za suyi tafiyar nan, amma sai gashi karami cikinsu wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa shi ya ɗauki hatsarin tafiyar ba tare da tunanin abinda zai je ya dawo ba.

Cikin nutsuwa Malamin ya shiga har gitsa gashin kan Jalaluldeen tare da yiwa lallausan baƙin gashin nasa rini da wata kala ja da kuma kuriya,

Yana gamawa ya ɗauki baƙin fenti ya shiga shafawa a saman ƙyakkyawar farar fuskar Abu Maleek, fuska mai tsananin kyau haiba da kuma kwarjini,

Fuskar da take Bara zana wa ƴan mata,

Few minutes fuskar Abu Maleek ta zama baƙa ƙirin, banda idanunsa da suke farare kuma manya, sai jajayen laɓɓansa da suke masu taushi da laushi,

Kana aka dawo hannayensa zuwa wuyansa, ana zuwa za’a buɗe ƙirjinsa yayi saurin damƙe hannun Malamin,

Kallonsa yayi yace.

“Ka bari a shafa har Nan saboda gudun samun matsala”

Shiru yayi baice komai ba, hakan yasa Malamin ƙara nufar ƙirjinsa zai zame rigar, bakin Abu Maleek na rawa da karkarwa yace.

“Stop”

Ya faɗa a lokacin da gaba ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa ya shiga langwaɓar da kansa gefe idanunsa suka shiga fitowa, 

Malamin kam sam bai lura da yanayin da Abu Maleek ya shiga ba, ya ƙara nufar ƙirjinsa karyar da wuya Abu Maleek yayi tare da buɗe baki yace.

“O’ohhhh”

Yana faɗin hakan ya zabura tare da shaƙe wuyan Malamin jikinsa duka tsuma yake da karkarwa, taɓe Baki Adams yayi tare da miƙewa ya fice daga cikin tirakar,

Sharefddeen ne ya miƙe tare kallon Abu Maleek yace.

“Let go of him, sake sa Jalaluldeen”

Wani kallo da Abu Maleek yayiwa Sharefdeen sai da yaji hantar cikinsa ta juya, da sauri kuma ya sakesa tare sayin baya,

Ganin yana ƙoƙarin yin kisa ne gashi kowa ya kasa ƙwatar Malamin daga hannun Abu Maleek,

Cikin tsayawa da kuma ɗaga Murya Oumuu-Ayman dake bakin ƙofa tace.

“JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL SAKE SA”

sakinsa Abu Maleek yayi tare da sulalewa a wajan ya zube saman ƙafafuwansa,

Ana sakin Malamin ya kwashi kayansa da sauri yabar wajan,

A hankali Oumuu-Ayman ta ƙarasa inda yake durƙoshe jikinsa na rawa tana zuwa ta zauna tare dasa hannunta ta jawosa saman cinyarta, 

Har zuwa lokacin jikinsa bai bar rawa ba, addu’a ta shigayi masa, tana shafa sumar kansa wacce aka ɓata da kala,

Idan ka kalli Abu Maleek a wannan lokacin zaka tabbatar cewa eh da gaske mahaukaci ne shi,

Irin masu dukan nan, Cikin kuka Queen Ayoola tace.

“Yanzu a haka za’a barsa yaje? Wannan wacce irin jarrabawa ce Ubangiji yake sanya mu cikinta ne?”

Ta ƙare maganar tana sakin Kuka, Mai Babban ɗaki wanda wacce tana zaune ko motsi ba tayi ba, tai gyaran murya tare da faɗin.

“Kowa yaje waje”

Queen Ayoola ce ta Miƙe, kana Bola sai kuma Junaid sai Shakiru da Sharefddeen, ya rage daga Otun sai Oumuu-Ayman da Mai Babban ɗaki,

A nan jikin Oumuu-Ayman bacci ya ɗauke sa, sai da yayi baccin awa guda sannan ya farka yana tashi Oumuu-Ayman ta bashi ruwa mai sanyi ta bashi yasha, kana ya gavatary da sallar zhur,

Nan aka fara shirya tafiya yayinda aka hana zuwa kowa yiwa Abu Maleek sallama,

A hankali ya tura ƙofar parlon Adams, yana tsaye hannunsa riƙe da File, kallo guda yayiwa Abu Maleek ya ɗauke kai,

Abu Maleek kam cikin soyayyyar ɗan uwan nasa ya nufi Adams, da niyyar ya rungomesa da sauri Adams yaja baya tare da ɗaga masa hannu yace.

“Mene ya kawo ka?”

Da mamaki Abu Maleek wanda ya zama mahaukacin gaske idan ba sani kayi ba yake duban Adams kafin yaja numfashi yace.

“I’m going now, nazu just to say i miss You Bro”

Murmushi Adams yayi kafin yace.

“Uhm! Kazo sace ni ne kamar yadda ka sace mun Mahaifiya tunda naga kai ba sonta kake ba”

Zare ido Abu Maleek yayi yana faɗin “sace Mami?”

“Yeah, of course koda yake mahaukaci like you babu abinda bazai iya ba, musamman yanzu  da sanyi zai fara hauka kuma sai Allah, ina jan kunanka Jalaluldeen duk inda ka kai mini mahaifiya ka gaggauta fito da ita, if not Uhm you have no idea akan abinda zan maka, mahaukacin banza”

Yana faɗin hakan ya shige cikin bedroom ɗinsa, 

“O’ohhh”

Shine abinda Abu Maleek ya samu zarafin faɗa, tsoro da tashin hankali ya bayyana a saman baƙar fuskarsa,

Juyawa yayi ya fita.

Sosai Oumuu-Ayman taci kuka ita ɗaya hakama Salimerh, Mai Babban ɗaki kam rungomesa tayi, bayan yaje ya ƙara duba King Tunde ya ɗauki sweet a hannunsa kana ya shiga mota aka fita dashi daga cikin Alaafin.

Kwanakin Julde biyar kenan, a cikin jejin

Yanzu ma tana tafe dafe da ƙirjinta idanunta cike da hawaye, ga yunwar da tayi mata illa,

A haka take dogara sandar tana lalubar hanya, gaba ɗaya zanin jikinta ya gutsire yayi kamar ƙaramin wando 3gauther,

Ga kan nan nata sai ƙyalli yake, yay wani babba tashi, sai jajayen laɓɓanta da suka ƙara wani jaa saboda taunewa da take,

Tazu dai-dai gaɓar wani ƙaton kogi ta sulale a wajan, sabida yunwa da ƙishin da take ji,

A hankali kuma ta rarrafa ta shiga lalubar Nagge tana jin wata kusa da ita, ta kafa bakinsa a nonon naggen ta fara zuƙa tana shaa, sai da tasha sosai, kamar daga sama kuma ta fara jiyo sautin bindigo alamar masu satar shanu sun kawo mata hari kenan, cikin kiɗima da kuma gigita ta fara ƙoƙarin neman wajan ɓoye, gashi babu idanu,

A haka take tafiya ba tare da sanin inda take nufa ba,

Ta ɗaga ƙafarta kenan zata sauke ji kake cindummmmm ta faɗa cikin tafkeken kogin da babu wanda yasan ida ya tsaya.

Miƙewa yayi daga zaman da yake, shigowar kenan cikin ƙasar Guinea, yayinda yaya da zango daga ɗan nesa da rugar Mahinjo,

Gaba ɗaya dashi da Sweet a galabaice suke, har baya iya buɗe idanunsa,

A wahalarce yake ɗaga ƙafarsa yana saukewa, kai tsaye kuma ya nufi inda yake hango wani haske na tashi, 

A haka ya isa gaɓar kogin cikin farin ciki ya zauna tare da sauke sweet, yana sauketa ta faɗa cikin ruwan ta shiga sha, farin ciki itama ya sauka akan fuskarta,

Abu Maleek a hankali ya sanya tafin hannunsa ya ɗebi ruwan yakai bakinsa, wani irin lumshe idanunsa yayi saboda daɗi da kuma sanyin ruwan da yaji,

Kasa ɗaurewar yayi ya Kafa bakinsa ya shiga shan ruwan, 

Yana ɗago kansa idanunsa ya sauka akan wani gawar ƙaramin yaro fari ƙyakƙyawa dake yawo saman ruwan,

Cike da tausayi ya runtse idanunsa abin kuma mamaki gaba ɗaya gawar ƙara kusanto inda Abu Maleek yake take,

Sweet ma tsayawa tayi tana karkaɗa jela,

A haka gawar tazo dai-dai inda Abu Maleek yake kai tsaye kuma ta shige jikinsa,

Ware idanunsa ya yi cike da tsoro saboda yadda ruwa ya kumbura cikin yaron Kallon fuskar yaron yayi, gashi fari ƙyakƙyawan gaske,

Ga laɓɓan yaron masu kyau wanda bai taɓa ganin irinsu ba, a hankali kuma rigar jikin yaron ta zame daga jikinsa tabi ruwa,

Igiyar dake ɗaure jikin yaron ta bayyana ba ƙaramin ɗauri akaiwa ƙirjin ba,

Sosai Abu Maleek abin ya bashi mamaki, babu mamaki kuma ɗaurin ƙirjin nasa ne ya sanya shi faɗa ruwan ya mutu.

Cike da tausayin yaron ya tallafo sa zuwa faffaɗan ƙirjinsa yana shafa fuskarsa, hannunsa ya ƙara a hancin yaron yaji numfashi na fita,

Julde kam cikin rashin sanin inda kanta take ta kama hannun Abu Maleek tare da mannawa ƙirjinta a ƙoƙarin ta na son cewa ya cire mata ƙullin kasa nononta ya fashe,

Cikin Zallar tausayin yaron Abu Maleek ya jawo yaron jikinsa sosai tare da ɗura hannunsa a kan igiyar ya shiga kuncewa, wata wahalalliyar ajjiyar zuciya Julde ta sauke saboda kunce ɗaurin da Abu Maleek yayi kafin kuma cak numfashinta ya tsaya da harbawa,

Cikin son taimakon yaron Abu Maleek ya mirgina yaron a ƙoƙarin sa na son danna masa cikin ruwan da yasha ya fita,

Cikin rashin Sa’a kuma idanunsa ya sauka akan…..

 *LAST FREE PAGE🥱*

      AUTHOR NOTE👇🏾

*ALLAHAMDULILLAH A NAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGES ƊIN ABU_MALEEK, WANDA YA KESON CI GABAN BOOK 1 2 3, ZAI BIYA 500 POSTING KULLUM SAFE DA YAMMA, GA MASU ƘARAMIN ƘARFI ZASU BIYA 300 AMMA POSTING IDAN ANYI YAU BA ZA’AI GOBE BA, VIA 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 GA ƳAN NIGER SUYI MAGANA TA WANNAN NUMBER 84506476, DAN ALLAH DAN ANNABI IDAN HAR VIP KIKE SON SHIGA MAGANA 500 ZAKI BIYA KIMIN ADALCI KI TURO MIN KUƊIN TA ASUSUN BANKI NA, SABODA BAN FIYA AMFANI DA KATIN WAYA BA, IDAN BABU BANKI AKWAI P.O.S  A KO’INA, MASU 300 MA HAKA SAI BABU YADDA ZA’AI SANNAN ZA’A TURA KATIN MTN*

*A KULLUM INA GODIYA GAREKU MASOYA NA, A DUK INDA KUKE FARIN CIKINKU SHI NE NAWA, A FITO A NUNA MIN ZALLAR SOYAYYA A BIYA KUƊIN ABU MALEEK ASHA KARATU, MACE MAI AJI BATA TSAYAWA JIRAN KAYAN SATA, MAI ZUCIYA KUMA AKE GAYAWA ABU BA MAI DUKIYA BA, DAN HAKA KI FIDDA KUƊI KI SIYA KISHA KARATU CIKIN NUTSUWA, DAN ALLAH IDAN BA SIYA ZAKI BA KADA KIYI MAGANA PLEASE*

1.ME ABU_MALEEK YA GANI?

2.ME ARƊO ZAI AIKATA WA JULDE NAN GABA?

3. MENENE TSAKANIN JARIRIN WAJAN HADIMA ZUBAIDA DA KUMA KING TUNDE?

4. WACECE TAKE SHIGAR HADIMA ZUBAIDA?

5. A INA QUEEN ROOMANA TAKE? DA GASKE JALALULDEEN NE YA ƊAUKE TA KO KUMA A’A?

6. MENE ZAI FARU BAYAN TAFIYAR ABU MALEEK?

7. WANNE HALI ABU MALEEK ZAI SHIGA NAN GABA?

8. MENE YA SANYA ABU MALEEK BAYA SON MALEEK?

9. WANNE IRIN ZANE NE A JIKIN ABU MALEEK?

UHM KADA KUYI MISSED KO HANZARTA BIYAN KUƊI DOMIN A CILLAKU CIKIN ORIGINAL ABU MALEEK GROUP.

NAGODE SOSAI DA SOYAYYA, DAGA LITTAFIN ABU MALEEK KUMA IN SHA ALLAH ZAN ƊAUKI HUTU, KOMA ZANYI RUBUTU SAI A WATTPAD.

  SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH DA ANNABI👏🏻👏🏻👏🏻 LAST FREE PAGES💃🏻✍🏽

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE